Ayuba 36:1-15
1
Elihu ya ci gaba,
2
“Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
3
Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.
4
Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.
5
“Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.
6
Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.
7
Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.
8
Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,
9
yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.
10
Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu.
11
In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
12
Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi.
13
“Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
14
Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.
15
Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu.
Settings