Irmiya 9:17-19
17
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo.
18
Bari su zo da sauri su yi kuka a kanmu sai idanunmu sun cika da hawaye giranmu kuma su jiƙe sharkaf.
19
An ji karar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Duba yadda muka lalace! Duba irin babban kunyar da muka sha! Dole mu bar ƙasar domin gidajenmu sun lalace.’ ”
Settings