Irmiya 52:12-15
12
A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.
13
Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima.
14
Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.
15
Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.
Settings