Irmiya 51:34-44
34
“Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu.
35
Bari abin da aka yi wa jikinmu yă kasance a bisa Babilon,” in ji mazaunan Sihiyona. “Bari jininmu yă kasance a kan waɗanda suke zama a Babilon,” in ji Urushalima.
36
Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “Duba, zan tsaya muku, zan ɗaukar muku fansa, zan sa tekunta kafe in kuma sa maɓulɓulanta su ƙafe.
37
Babilon za tă zama tarin juji, wurin zaman diloli, abin ƙyama da abar ba’a, inda ba kowa.
38
Mutanenta duk suna ruri kamar zakoki, suna gurnani kamar ’ya’yan zaki.
39
Amma sa’ad da aka farkar da su, zan yi musu biki in sa su sha su bugu, domin yi sowa da dariya, sa’an nan su shiga barcin da ba za su farka ba,” in ji Ubangiji.
40
“Zan sauko da su kamar tumaki zuwa mayanka, kamar raguna da bunsurai.
41
“Yadda za a ci Sheshak, taƙamar duniya duka za tă daina! Babilon za tă zama abar ƙyama a cikin al’ummai!
42
Teku zai malalo a kan Babilon, raƙumansa masu hauka za su rufe ta.
43
Garuruwanta sun zama abin kufai, za tă zama hamada inda ba ruwa, ƙasar da ba mazauna, ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta.
44
Zan hukunta Bel a Babilon, in sa ya yi aman abin da ya haɗiye. Ƙasashe ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Katangan Babilon kuwa za tă rushe!
Settings