Irmiya 41:5-10
5
sai ga mutane tamanin daga Shekem, Shilo da Samariya suka zo da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage, suka kawo hadayun gari da turare tare da su a gidan Ubangiji.
6
Ishmayel ɗan Netaniya ya fito daga Mizfa don yă sadu da su. Sa’ad da ya sadu da su, sai ya ce, “Ku zo wurin Gedaliya ɗan Ahikam.”
7
Da suka shiga cikin birni, sai Ishmayel ɗan Netaniya da mutanen da suke tare da shi suka karkashe su suka zubar a rijiya.
8
Amma goma daga cikinsu suka ce wa Ishmayel, “Kada ka kashe mu, muna da alkama da sha’ir, mai da kuma zuma, a ɓoye a gona.” Saboda haka ka bar mu kada ka kashe mu tare da sauran.
9
To, rijiyar da ya zubar da gawawwakin mutanen da ya kashe tare da ta Gedaliya ita ce wadda Sarki Asa ya haƙa a matsayin kāriya saboda Ba’asha sarkin Isra’ila. Ishmayel ɗan Netaniya ya cika ta da gawawwaki.
10
Ishmayel ya mai da dukan sauran mutanen da suke Mizfa bayi ’ya’yan sarki mata tare da dukan sauran da aka bari a can, waɗanda Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Ishmayel ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya tashi don yă haye zuwa wurin Ammonawa.
Settings