Skip to content
Irmiya 37:1-10

Irmiya 37:1-10

1
Nebukadnezzar sarkin Babilon ya naɗa Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda; ya yi mulki a madadin Yehohiyacin ɗan Yehohiyakim.
2
Shi da masu yin masa hidima da mutanen ƙasar ba su kula da maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya annabi ba.
3
Sai sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya tare da firist nan Zefaniya ɗan Ma’asehiya da wannan saƙo cewa, “Ina roƙonka ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnmu saboda mu.”
4
To, fa, Irmiya ya sami ’yancin kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a riga an sa shi a kurkuku ba.
5
Sojojin Fir’auna suka fita daga Masar, sa’ad da Babiloniyawa waɗanda suke ƙawanya wa Urushalima suka ji labari game da su, sai suka janye daga Urushalima.
6
Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa,
7
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar.
8
Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’
9
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba!
10
Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options