Skip to content
Irmiya 36:27-32

Irmiya 36:27-32

27
Bayan sarki ya ƙone littafin da ya ƙunshi maganar da Baruk ya rubuta daga shibtar Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
28
“Ka ɗauki wani littafi ka rubuta a kansa dukan maganar da littafi na farin ya ƙunsa, wanda Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone.
29
Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?”
30
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa game da Yehohiyakim sarkin Yahuda. Ba zai kasance da wani wanda zai zauna a kan gadon sarautar Dawuda ba; za a jefar da gawarsa ta sha zafi da rana da dare kuma ta sha matsanancin sanyi.
31
Zan hukunta shi da kuma ’ya’yansa da masu hidimarsa saboda muguntarsu; zan kawo kowace masifar da na furta a kansu da kuma waɗanda suke zama a Urushalima da na Yahuda, domin sun ƙi su saurara.’ ”
32
Sai Irmiya ta ɗauko wani littafi ya ba wa Baruk ɗan Neriya marubuci, kuma yayinda Irmiya yake shibtawa, Baruk ya rubuta a littafin dukan maganar da take a littafin da Yehohiyakim sarkin Yahuda ya ƙone. Ya kuma ƙara ire-iren maganganun nan a kansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options