Irmiya 32:1-6
1
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga Ubangiji a shekara ta goma ta Zedekiya sarkin Yahuda, wanda ya kasance shekara ta goma sha takwas ta Nebukadnezzar.
2
Sojojin sarkin Babilon a lokacin suna ƙawanya wa Urushalima annabi Irmiya kuwa yana a tsare a sansanin matsara a fadar Yahuda.
3
Zedekiya sarkin Yahuda fa ya sa shi a kurkuku yana cewa, “Don me kake yin annabci? Ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa cinye ta.
4
Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa.
5
Zai kai Zedekiya Babilon, inda zai zauna har sai ya magance shi, in ji Ubangiji. In ka yi yaƙi da Babiloniyawa, ba za ka yi nasara ba.’ ”
6
Irmiya ya ce, “Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
Settings