Irmiya 28:13-17
13
“Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe.
14
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ”
15
Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.
16
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”
17
A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.
Settings