Irmiya 27:11-15
11
Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”
12
Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.
13
Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?
14
Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.
15
‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”
Settings