- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Irmiya 22:1-3
Kira ga sarki ya yi adalci
1
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ka gangara zuwa fadan sarkin Yahuda ka yi shelar wannan saƙo a can ka ce,
2
‘Ka ji maganar Ubangiji, ya sarkin Yahuda, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda, kai, da fadawanka da mutanenka waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.
3
Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.
A cikin nassin nan
- Su wane
- Ina
- Yaushe
- About
Duba kuma
Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka
Irmiya 21:12
Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.daga aya ta 3Irmiya 22:17
“Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.”daga aya ta 3Mika 6:8
Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.daga aya ta 3Yaƙub 1:27
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.daga aya ta 3Ezekiyel 22:7
A cikinki sun rena mahaifi da mahaifiya; a cikinki sun zalunci baƙo suka wulaƙanta maraya da gwauruwa.daga aya ta 3Luka 1:32
Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,daga aya ta 2Ishaya 1:15
Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!daga aya ta 3Ishaya 1:20
amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa, za a kashe ku da takobi.” Ni Ubangiji na faɗa.daga aya ta 3Malaki 3:5
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.daga aya ta 3Zakariya 7:9
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna.daga aya ta 3Zakariya 7:11
“Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.daga aya ta 3Irmiya 34:2
“Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka tafi wurin Zedekiya sarkin Yahuda ka faɗa masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga sarkin Babilon, zai kuwa ƙone ta.daga aya ta 1
Inda wannan ya faru

Bayanin Nazari
Settings