Skip to content
Irmiya 21:11-14

Irmiya 21:11-14

11
“Ban haka ma, ka faɗa wa gidan sarauta na Yahuda cewa, ‘Ku saurari maganar Ubangiji;
12
Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya; ku kuɓuta daga hannun mai danniya wannan da aka yi wa fashi in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci babu wanda zai kashe ta.
13
Ina gāba da ku, mazaunan Urushalima, ku da kuke zama a bisa wannan kwari kan dutsen da yake a fili, in ji Ubangiji ku da kuke cewa, “Wa zai iya yaƙe mu? Wa zai iya shiga mafakarmu?”
14
Zan hukunta ku gwargwadon ayyukanku, in ji Ubangiji. Zan sa wuta a kurminku da za tă cinye kome da yake kewaye da ku.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options