Irmiya 16:1-9
1
Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Kada ka yi aure ka haifi ’ya’ya maza da mata a wannan wuri.”
3
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa game da ’ya’ya maza da matan da aka haifa a wannan ƙasa da kuma game da matan da suke iyayensu da suke mazan da iyayensu.
4
“Za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi kuka dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba, amma za a bar su a juji. Takobi da yunwa ne za su hallaka su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji na duniya.”
5
Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kada ka shiga gidan da akwai abincin makoki; kada ka tafi ka yi makoki ko ka nuna juyayi, domin na janye albarkata, ƙaunata da tausayina daga wannan mutane,” in ji Ubangiji.
6
“Manya da ƙanana duka za su mutu a wannan ƙasa. Ba za a binne su ba, ba kuwa za a yi makokinsu ba, kuma ba wanda zai tsaga kansa ko ya aske kansa saboda su.
7
Ba wanda zai ba da abinci don yă ta’azantar da waɗanda suke makoki saboda matattu, kai, ko saboda mahaifi ko mahaifiya ma ba kuwa wani da zai ba da abin sha don yă ta’azantar da su.
8
“Kada kuma ka shiga gidan da ake biki ka zauna don ci da sha.
9
Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa a idanunka da kuma a kwanakinka zan kawo ƙarshen muryar farin ciki da murna da kuma muryoyin amarya da ango a wannan wuri.
Settings