Irmiya 11:18-20
18
Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi.
19
Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”
20
Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata.
Settings