Skip to content
Irmiya 11:1-8

Irmiya 11:1-8

1
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.
2
“Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima.
3
Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba,
4
zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.
5
Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”
6
Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.
7
Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.”
8
Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options