Skip to content
Yaƙub 3:2-10

Yaƙub 3:2-10

2
Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.
3
Sa’ad da muka sa linzamai a bakunan dawakai don mu sa su yi mana biyayya, mukan iya bin da dabbar gaba ɗaya.
4
Ko kuwa misali, mu dubi jiragen ruwa, mana. Ko da yake suna da girma ƙwarai kuma iska mai ƙarfi ce take tura su, ana tuƙa su da ɗan ƙaramin sandan ƙarfe ne zuwa duk inda mai tuƙin jirgin yake so.
5
Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana.
6
Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.
7
Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa,
8
amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
9
Da harshe mukan yabi Ubangijinmu da kuma Ubanmu, da shi kuma muke la’antar mutane, waɗanda aka halitta a kamannin Allah.
10
Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. ’Yan’uwana, wannan bai kamata yă zama haka ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options