Ishaya 7:1-6
1
Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.
2
Sai fa aka faɗa wa gidan Dawuda cewa, “Aram ya haɗa kansa da Efraim”; saboda haka zuciyar Ahaz da ta mutanensa suka firgita, sai ka ce itatuwa a kurmin da iska ta girgiza.
3
Sai Ubangiji ya ce wa Ishaya, “Fita, kai da ɗanka Sheyar-Yashub, don ku sadu da Ahaz a ƙarshen wuriyar da take kawo ruwa daga Tafkin Tudu, a hanyar Filin Mai Wanki.
4
Ka faɗa masa, ‘Ka yi hankali, ka natsu kada kuma ka ji tsoro ko ka damu, kada ka ji tsoron fushin sarki Rezin da na Aram da na ɗan Remaliya, ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin ’yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.
5
Aram, Efraim da ɗan Remaliya sun ƙulla maƙarƙashiya, suna cewa,
6
“Bari mu kai wa Yahuda hari; bari mu yayyage su mu rarraba su a tsakaninmu, mu naɗa Tabeyel sarki a kansu.”
Settings