Skip to content
Ishaya 66:1-6

Ishaya 66:1-6

1
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance?
2
Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata.
3
Amma duk ya miƙa hadayar bijimi yana kama da wanda ya kashe mutum, kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago, kamar wanda ya karye wuyan kare; duk wanda ya miƙa hadaya ta gari yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade, kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni, kamar wanda yake bauta gunki ne. Sun zaɓi hanyoyinsu, rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;
4
saboda haka ni ma zan aukar musu da masifa mai zafi in kuma kawo musu abin da suke tsoro. Gama sa’ad da na yi kira, ba wanda ya amsa, sa’ad da na yi magana, ba wanda ya saurara, Sun aikata mugunta a idona suka kuma zaɓa abin da ba na jin daɗi.”
5
Ku ji maganar Ubangiji, ku da kuke rawar jiki ga maganarsa, “’Yan’uwanku da suke ƙinku, suna kuma ware ku saboda sunana, sun ce, ‘Bari a ɗaukaka Ubangiji, don mu ga farin cikinku!’ Duk da haka za su sha kunya.
6
Ku ji wannan hayaniya daga birni, ku ji surutu daga haikali! Amon Ubangiji ne yana sāka wa abokan gābansa abin da ya dace da su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options