Ishaya 62:1-7
1
Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba, saboda Urushalima ba zan huta ba, sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya, cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.
2
Al’ummai za su ga adalcinki, sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki; za a kira ki da sabon suna sunan da bakin Ubangiji zai ambata.
3
Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji, rawanin sarauta a hannun Allahnki.
4
Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba, ko a kira ƙasarki Kango. Amma za a ce da ke Hefziba ƙasarki kuma Bewula; gama Ubangiji zai ji daɗinki, ƙasarki kuma za tă yi aure.
5
Kamar yadda saurayi kan auri yarinya, haka ’ya’yanki maza za su aure ki; kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa, haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.
6
Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,
7
kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.
Settings