Skip to content
Ishaya 61:4-9

Ishaya 61:4-9

4
Za su sāke gina kufai na dā su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa; za su sabunta biranen da aka rurrushe da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.
5
Baƙi za su yi kiwon garkunanki; baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.
6
Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.
7
A maimakon kunyarsu mutanena za su sami rabi riɓi biyu, a maimakon wulaƙanci za su yi farin ciki cikin gādonsu; ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu, da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.
8
“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci; na ƙi fashi da aikata laifi. Cikin adalcina zan sāka musu in kuma yi madawwamin alkawari da su.
9
Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai ’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options