Ishaya 57:3-13
3
“Amma ku, ku matso nan, ku ’ya’ya maza na masu sihiri, ku zuriyar mazinata da karuwai!
4
Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata?
5
Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oak da kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa; kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffuka da kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.
6
Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku; su ɗin, su ne rabonku. I, gare su kuka kwarara hadayu na sha kuka kuma miƙa hadayu na gari. Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?
7
Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo; a can kuka haura don ku miƙa hadayunku.
8
A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofi kuka kafa alamun gumakanku. Kuka yashe ni, kuka kware gadonku, kuka kwanta a kansa kuka fadada shi; kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu, kuka dubi tsiraicinsu.
9
Kuka tafi wurin Molek da man zaitun kuka kuma riɓaɓɓanya turarenku. Kuka aika jakadunku can da nisa; kuka gangara zuwa cikin kabari kansa!
10
Kuka gaji cikin dukan al’amuranku, amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’ Kuka sami sabuntar ƙarfinku, ta haka ba ku suma ba.
11
“Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsoro har kuka yi mini ƙarya, ba ku kuma tuna da ni ba balle ku yi tunanin wannan a zukatanku? Ba don na daɗe ina shiru ba ne ya sa ba kwa tsorona?
12
Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku, ba kuwa za su amfane ku ba.
13
Sa’ad da kuka nemi taimako, bari tarin gumakanku su cece ku! Iska za tă kwashe dukansu tă tafi, ɗan numfashi kawai zai hura su. Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa zai gāji ƙasar ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
Settings