Ishaya 51:17-23
17
Ki farka, ki farka! Ki tashi, ya Urushalima, ke da kika sha daga hannun Ubangiji kwaf na fushinsa, ke da kika shanye har ƙasar kwaf kwaf da ya sa mutane suna tangaɗi.
18
Cikin dukan ’ya’yan da ta haifa; cikin dukan ’ya’yan da ta yi reno babu wani da zai kama hannunta.
19
Waɗannan masifu riɓi biyu sun auko miki, wa zai ta’azantar da ke? Lalaci da hallaka, yunwa da takobi, wa zai ƙarfafa ki?
20
’Ya’yanki sun sume; sun kwanta kusurwar kowane titi, kamar barewar da aka kama da tarko. Sun cika da fushin Ubangiji da kuma tsawatawar Allahnki.
21
Saboda haka ki ji wannan, ke mai wahala, wadda ta bugu, amma ba da ruwan inabi.
22
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Allahnki, wanda ya kāre mutanensa, “Duba, na ƙwace daga hannunki kwaf da ya sa ki tangaɗi; daga wannan kwaf, kwaf na fushina, ba za ki ƙara sha ba.
23
Zan sa shi a hannuwan masu gwada miki azaba, waɗanda suke ce miki, ‘Fāɗi rubda ciki don mu iya taka a kanki.’ Kika kuma mai da bayanki kamar ƙasa, kamar titin da ake takawa a kai.”
Settings