Skip to content
Ishaya 49:1-7

Ishaya 49:1-7

1
Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai; ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa. Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni; tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
2
Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi, cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni; ya sa na zama kamar kibiya mai tsini ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.
3
Ya ce mini, “Kai bawana ne, Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”
4
Amma na ce, “Na yi aiki a banza; na kashe duk ƙarfina a banza da wofi. Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji, ladana kuma tana a wurin Allahna.”
5
Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina
6
ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
7
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options