Ishaya 42:18-25
18
“Ka ji, kai kurma; duba, kai makaho, ka kuma gani!
19
Wane ne makaho in ba bawana ba, da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba? Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni, makaho kamar bawan Ubangiji?
20
Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba; kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”
21
Yakan gamsar da Ubangiji saboda adalcinsa ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.
22
Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima, an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku. Sun zama ganima, babu wani da zai kuɓutar da su; an mai da su ganima, ba wanda zai ce, “Mayar da su.”
23
Wane ne a cikinku zai saurari wannan ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?
24
Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima? Ba Ubangiji ba ne, wanda kuka yi wa zunubi? Gama ba su bi hanyoyinsa ba; ba su yi biyayya da dokarsa ba.
25
Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa, yaƙi mai tsanani. Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba; ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.
Settings