Ishaya 41:1-3
1
“Ku yi shiru a gabana, ku tsibirai! Bari al’ummai su sabunta ƙarfinsu! Bari su zo gaba su yi magana; bari mu sadu a wurin shari’a.
2
“Wa ya zuga wannan daga gabas, yana kiransa cikin adalci ga yin hidima? Ya miƙa masa al’ummai ya kuma yi nasara da sarakuna a gabansa. Ya mai da su ƙura da takobinsa, zuwa inda iska ke hurawa ta wurin bugun da ya yi musu.
3
Ya fafare su ya kuma yi tafiyarsa lafiya ƙalau, a hanyar da ƙafafunsa ba su taɓa bi ba.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings