Skip to content
Ishaya 37:9-13

Ishaya 37:9-13

9
To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana.
10
“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’
11
Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne?
12
Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar?
13
Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”

Duba kuma

Sauran wuraren da Nassi ya faɗi haka

  • Farawa 11:31

    Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
    daga aya ta 12
  • Ishaya 36:15

    Kada ku bar Hezekiya ya rarashe ku ku dogara ga Ubangiji sa’ad da ya ce, ‘Tabbatacce Ubangiji zai cece mu; ba za a ba da wannan birni a hannun sarkin Assuriya ba.’
    daga aya ta 10
  • Ishaya 36:20

    Wanne cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa daga gare ni? Yaya kuwa Ubangiji zai iya ceci Urushalima daga hannuna?”
    daga aya ta 10
  • 2 Sarakuna 17:6

    A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.
    daga aya ta 11
  • Ishaya 36:18

    “Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ Allahn wata al’umma ya taɓa ceci ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?
    daga aya ta 11
  • 2 Sarakuna 18:11

    Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.
    daga aya ta 12
  • 2 Sarakuna 19:12

    Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?
    daga aya ta 12
  • Ayyukan Manzanni 7:2

    Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.
    daga aya ta 12
  • 1 Sama’ila 23:27

    sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”
    daga aya ta 9
  • 1 Sama’ila 23:28

    Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.
    daga aya ta 9
  • Ishaya 18:1

    Kaiton ƙasar da ake jin ƙarar fikafikai a bakin kogunan Kush,
    daga aya ta 9
  • Ishaya 20:5

    Waɗanda suka dogara ga Kush suka yi taƙama da Masar za su ji tsoro su kuma sha kunya.
    daga aya ta 9

Inda wannan ya faru

Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options