Ishaya 36:4-9
4
Sai sarkin yaƙin ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya. “ ‘Ga abin da babban sarki, sarkin Assuriya, ya faɗa. A kan me kake dangana wannan ƙarfin halinka?
5
Ka ce kana da dabara da kuma ƙarfin mayaƙa, amma kana magana banza ce kawai. Ga wa ka dogara, da kake tayar mini?
6
Yanzu duba, kana dogara ga Masar, wannan ɗan tsinken kyauron dogarawa, wanda zai soki hannun mutum yă kuma ji masa rauni in ya dangana a kansa! Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara da shi.
7
Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”?
8
“ ‘Yanzu fa, bari in yi ciniki da maigidana, sarki Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sa mahaya a kansu!
9
Yaya za ka ƙi hafsan mafi ƙanƙanci na hafsoshin maigidana, ko da yake kana dogara ga Masar don kekunan yaƙi da mahayan dawakai?
Settings