Ishaya 32:10-14
10
Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.
11
Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.
12
Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau don ’ya’yan inabi
13
da kuma don ƙasar mutanena, da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma, I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.
14
Za a ƙyale kagarar, a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya; mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada, jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,
Settings