Ishaya 29:9-12
9
Ku firgita ku kuma yi mamaki, ku makance kanku ku kuma zama a makance; ku bugu, amma ba da ruwan inabi ba, ku yi tangaɗi, amma ba daga barasa ba.
10
Ubangiji ya kawo muku barci mai nauyi, Ya rufe idanunku (annabawa); ya rufe kawunanku (masu duba).
11
Gare ku duk wannan wahayi ba kome ba ne sai dai maganganun da aka rufe a cikin littafi. In kuma kun ba da littafin ga wani wanda zai iya karanta, kuka kuma ce masa, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ba zan iya ba; an rufe shi.”
12
Ko kuwa in kun ba da littafin ga wani wanda ba zai iya karantawa ba, kuka kuma ce, “Karanta wannan, muna roƙonka,” zai amsa ya ce, “Ban iya karatu ba.”
Settings