Skip to content
Ishaya 2:12-22

Ishaya 2:12-22

12
Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su),
13
domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,
14
domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi,
15
domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi,
16
domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.
17
Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,
18
za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
19
Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
20
A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu.
21
Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
22
Ku daina dogara ga mutum, wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa. Wace daraja gare shi?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options