Ibraniyawa 7:12-19
12
Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma.
13
Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade.
14
Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba.
15
Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.
16
Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa.
17
Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
18
Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani
19
(gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.
Settings