Skip to content
Ibraniyawa 7:1-17

Ibraniyawa 7:1-17

1
Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna,
2
Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne.
3
Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada.
4
Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima!
5
Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne.
6
Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura.
7
Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka.
8
Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai.
9
Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim,
10
wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.
11
Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna.
12
Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma.
13
Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade.
14
Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba.
15
Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.
16
Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa.
17
Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options