Tsallake zuwa abun ciki
Ibraniyawa 6:9-12

Ƙarfafawa da Tabbacin Ceto

Ibraniyawa 6:9-12
9
Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi.
10
Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.
11
Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku.
12
Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options