Skip to content
Ibraniyawa 6:13-17

Ibraniyawa 6:13-17

13
Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,
14
cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”
15
Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.
16
In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama.
17
Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options