Skip to content
Ibraniyawa 5:1-4

Ibraniyawa 5:1-4

1
Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.
2
Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.
3
Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.
4
Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options