Ibraniyawa 5:1-2
1
Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.
2
Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.