Ibraniyawa 2:11-17
11
Da shi wanda yake tsarkake mutane da kuma su waɗanda ake tsarkakewa duk ’yan iyali ɗaya ne. Saboda haka Yesu ba ya kunyan kiransu ’yan’uwansa.
12
Ya ce, “Zan sanar da sunanka ga ’yan’uwana; a gaban jama’a zan rera yabonka.”
13
Har wa yau ya ce, “Zan dogara gare shi.” Ya kuma ce, “Ga ni, da ’ya’yan da Allah ya ba ni.”
14
Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis
15
ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.
16
Gama tabbatacce ba mala’iku ne ya taimaka ba, sai dai zuriyar Ibrahim.
17
Saboda wannan dole a mai da shi kamar ’yan’uwansa ta kowace hanya, domin yă zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.
Settings