Skip to content
Farawa 6:17-18

Farawa 6:17-18

17
Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.
18
Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options