Skip to content
Farawa 50:1-7

Farawa 50:1-7

1
Yusuf kuwa ya fāɗa a kan mahaifinsa, ya yi kuka a kansa, ya kuma sumbace shi.
2
Sa’an nan Yusuf ya umarci masu maganin da suke yin masa hidima, su shafe mahaifinsa Isra’ila da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe shi da maganin hana ruɓa.
3
Suka ɗauki kwana arba’in cif suna yin wannan, gama kwanakin da ake bukata ke nan don shafewa da maganin hana ruɓa. Masarawa kuwa suka yi makoki dominsa kwana saba’in.
4
Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa,
5
‘Mahaifina ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, “Ina gab da mutuwa, ka binne ni a kabarin da na haƙa wa kaina a ƙasar Kan’ana.” Yanzu fa bari in haura in binne mahaifina, sa’an nan in dawo.’ ”
6
Fir’auna ya ce, “Haura ka binne mahaifinka, kamar yadda ya sa ka rantse za ka yi.”
7
Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options