Skip to content
Farawa 45:1-15

Farawa 45:1-15

1
Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.
2
Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.
3
Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
4
Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
5
Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.
6
Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
7
Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.
8
“Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.
9
Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.
10
Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai, ’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi.
11
Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’
12
“Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku.
13
Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.”
14
Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka.
15
Ya sumbaci dukan ’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai ’yan’uwansa suka yi masa magana.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options