Skip to content
Farawa 29:23-31

Farawa 29:23-31

23
Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki ’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.
24
Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa ’yarsa tă zama mai hidimarta.
25
Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
26
Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da ’ya ƙarama aure kafin ’yar fari.
27
Ka gama makon amaryanci na ’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”
28
Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi ’yarsa Rahila tă zama matarsa.
29
Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa ’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.
30
Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.
31
Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options