Farawa 26:12-17
12
Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi.
13
Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
14
Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa.
15
Saboda haka dukan rijiyoyin da bayin mahaifinsa suka haƙa a kwanakin da mahaifinsa Ibrahim yake da rai, Filistiyawa sun toshe su, suka kuma ciccike su da ƙasa.
16
Sai Abimelek ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu; ka fi ƙarfinmu.”
17
Saboda haka Ishaku ya fita daga can, ya yi sansani a Kwarin Gerar, ya kuma zauna a can.
Settings