Farawa 18:16-22
16
Sai mutanen suka tashi suka nufi Sodom, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya, ya yi bankwana da su.
17
Sai Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin yi?
18
Lalle Ibrahim zai zama al’umma mai girma da kuma mai iko, kuma ta wurinsa dukan al’umman duniya za su sami albarka.
19
Saboda na zaɓe shi don yă umarci ’ya’yansa da iyalinsa a bayansa su kiyaye hanyoyin Ubangiji, ta wurin yin abin da yake daidai da kuma yin adalci, domin Ubangiji ya aikata abin da ya yi wa Ibrahim alkawari.”
20
Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,
21
zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”
22
Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji.
Settings