Galatiyawa 5:13
Ana nuna aya 13 tare da mahallin da ke kewaye.
10
Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.
11
’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.
12
Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!
13
Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.
14
Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
15
In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.
16
Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba.
Settings