Skip to content
Galatiyawa 3:6-14

Galatiyawa 3:6-14

6
Ku dubi Ibrahim mana, “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
7
Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata, ’ya’yan Ibrahim ne.
8
Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Al’ummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yă yi cewa, “Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinka.”
9
Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.
10
Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”
11
A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
12
Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
13
Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”
14
Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options