Ezra 5:11-15
11
Wannan ita ce amsar da suka ba mu. “Mu bayin Allah na sama da ƙasa ne, muna sāke gina haikalin da aka gina tun shekaru da yawa da suka wuce, da wani babban sarkin Isra’ila ya gina ya kuma gama.
12
Amma domin kakanninmu sun ɓata wa Allah na sama rai, sai ya bari suka fāɗa cikin hannun Nebukadnezzar mutumin Kaldiya, sarkin Babilon, wanda ya rushe wannan haikali, ya kuma kwashe mutane zuwa Babilon.
13
“Duk da haka, a shekara ta farko ta mulkin Sairus sarkin Babilon, Sarki Sairus ya ba da umarni cewa a sāke gina wannan gidan Allah.
14
Ya kuma kwashe kwanonin zinariya da azurfa na gidan Allah daga haikalin Babilon waɗanda Nebukadnezzar ya kwasa daga haikali a Urushalima. Sa’an nan sarki Sairus ya ba wa wani mutum mai suna Sheshbazzar umarni wanda ya sa ya zama gwamna,
15
ya ce masa, ‘Ka kwashe kayan nan ka je ka zuba su a cikin haikalin Allah a Urushalima. Ka kuma sāke gina gidan Allah a wurin da yake a dā.’
Settings