Ezra 3:2-6
2
Sai Yeshuwa ɗan Yozadak da sauran firistoci, da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da abokan aikinsa, suka fara gina bagaden Allah na Isra’ila don miƙa hadaya ta ƙonawa bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa mutumin Allah.
3
Duk da tsoron da suke ji na mutanen da suke kewaye da su, sun gina bagaden a wurinsa, suka kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagaden ga Ubangiji safe da yamma.
4
Bisa ga abin da yake a rubuce kuma, suka yi biki Bikin Tabanakul, suka miƙa hadayu kowace rana gwargwadon yawan hadayun da ake bukata.
5
Bayan wannan, suka miƙa hadayu na ƙonawa yadda aka saba. Suka miƙa hadayu na Sabon Wata, da hadayu na bukukkuwan Ubangiji, da kuma hadayun da aka bayar da yardar rai ga Ubangiji.
6
A ranar farko ta watan bakwai, sai suka fara miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko da yake ba a riga an aza harsashin ginin haikalin Ubangiji ba.
Settings