Skip to content
Ezekiyel 8:9-16

Ezekiyel 8:9-16

9
Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”
10
Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.
11
A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
12
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ”
13
Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
14
Sa’an nan ya kawo ni mashigin arewa na ƙofar gidan Ubangiji, sai na ga mata zaune a can, suna makokin Tammuz.
15
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga wannan? Za ka ga abubuwan da suke masu banƙyama fiye da wannan.”
16
Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options