Ezekiyel 8:7-13
7
Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.
8
Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.
9
Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”
10
Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.
11
A gabansu ga dattawa saba’in na gidan Isra’ila tsaye a cikinsu, Ya’azaniya ɗan Shafan kuwa yana tsaye a cikinsu. Kowa yana da farantin ƙona turare a hannunsa, tulin hayaƙin turare mai ƙanshi ya tunnuƙe zuwa sama.
12
Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da dattawan gidan Isra’ila suke yi a cikin duhu, kowa yana a ɗakin tsafin gunkinsa? Suna cewa, ‘Ubangiji ba ya ganinmu; Ubangiji ya yashe ƙasar.’ ”
13
Ya kuma ce, “Za ka gan su suna yin abubuwan da suka fi waɗannan banƙyama.”
Settings