Ezekiyel 7:5-13
5
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Masifa! Masifar da ba a taɓa gani ba tana zuwa.
6
Ƙarshe ya zo! Ƙarshe ya zo! Ya farka a kanki. Ga shi, ya zo!
7
Ƙaddara ta auko miki, ya ke wadda ke zama cikin ƙasar. Lokaci ya yi, rana ta gabato; akwai fargaba, ba farin ciki ba, a kan duwatsu.
8
Ina gab da fasa hasalata a kanki in kuma aukar da fushina a kanki; zan shari’anta ke bisa ga halinki in kuma sāka miki saboda dukan ayyukanki masu banƙyama.
9
Ba zan dube ki da tausayi ko in ƙyale ke ba; zan sāka miki bisa ga halinki da kuma ayyukan masu banƙyama a cikinki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji wanda yake bugunki.
10
“ ‘Ga shi ranar ta zo! Ta iso! Ƙaddararki ta keto, sandar ta yi toho, girman kai ya yi fure!
11
Rikici ya yi girma ya zama sandar da za a hukunta mugunta; babu wani daga cikin mutanen da za a bari, babu wani dukiyarsu da za a bari, babu wani abin amfani.
12
Lokaci ya yi! Ranar ta gabato! Kada mai saya ya yi farin ciki ko kuwa mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama hasala tana a kan dukan jama’a.
13
Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba muddin dukansu suna da rai, gama ba za a sauya wahayin da ya shafi dukan jama’a ba. Saboda zunubansu, babu ɗayansu da zai adana ransa.
Settings